IQNA

23:46 - August 03, 2018
Lambar Labari: 3482858
Bangaren kasa da kasa, an kame Salim Saimur wani dan liken asirin Isra'ila a Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jami'an tsaro sun kame wani jami'in liken asirin Isra'ila a Wahran.

Bayanin ya ce an kame wannan mutum ne a lokacin da yake daukar hotunan wasu muhimman wurare na soji masu masu matukar hadari, da nufin aikewa da su zuwa ga Isra'ila.

Salim Saimur dan shekaru 26 da haihuwa dan asalin kasar ta Aljeriya ne, kuma yana aiki ne a wani otel a kasar, kuma ta wannan hanyar ne yake samun tuntuba tsakaninsa da yahudawa.

3735513

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، muhimman ، otel ، Aljeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: