IQNA

Majalisar Musulmin Kenya Ta Nuna Damuwa Kan Karuwar Cin Hanci A Kasar

23:47 - August 05, 2018
Lambar Labari: 3482865
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukancin hanci da rashawa a kasar a cikin lokutan baya-bayan nan.

Wannan ya zo ne bayan wani zama da mambobin majalisar suka gudanar, inda suka bukaci gwamnatin kasar ta Kenya da ta dauki tsauraran matakai na shiga kafar wando daya da duk wanda aka samu da laifin barnata dukiyar kasa, ko halasta kudin haram, ko karbar cin hanci da rashawa.

Alhaj Shaban Bakari, shugaban majalisar muuslmin ya bayyana cewa, musulmi Kenya suna goyon bayan daukar duk wani mataki da gwamnati za ta yi na yaki da cin hanci da rashawa da wwure kudaden jama’a, domin hakan ya bayar da damar habbaka tattalin arzikin kasar.

3735912

 

captcha