IQNA

23:55 - August 06, 2018
Lambar Labari: 3482868
Bangaren kasa da kasa, a hajjin bana za a raba robobin ruwan zamzam guda miliyan bakawai da dubu dari biyar ga alhazai.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Arab News ta habarta cewa, hukuma da ke kula da rijar zamzam a aikin hajjin bana zata raba robobin ruwan zamzam guda miliyan bakawai da dubu dari biyar ga alhazai masu sauke farali.

Mutane da dama ne suke gudanar da aiki wurin da ake dibar ruwan na zamzam a kowace sheakara a lokacin aikin hajji a karkashin hukumar da ke kula da wurin.

Dubban alhazai da suke zuwa daga kasashen duniya suna daukar ruwan zamzam suna tafiya da shi zuwa kasashensu domin samun albarka da ke tattare da wannan ruwa mai tarihi.

3736436

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: