IQNA

Horo Kan Ilmomin Addinin Musulunci A Austria

23:54 - August 07, 2018
Lambar Labari: 3482872
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar nazarin addinin musulunci ta Iman da ke kasar Austria za ta gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmomin musulunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, nan ba da jimawa ba babbar cibiyar nazarin addinin musulunci ta Iman da ke birnin Vienna na kasar Austria za ta fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmomin musulunci da za a iya bayar da diiri a kansa.

Wannan shiri dai zai kunshi daukar laccoci ne daga kwararun malamai masana kan addinin muslunci, wadanda za su rika gabatar da lacca da kuma bayar da makalolinsu ga mahalarta horon.

Wadanda za su halarci shirin dai dole ne shekarunsu kada su haura arbain, kamar yadda kuma shirin zai dauki lokaci ana gudanar da shi bisa tsarin da aka yi, daga karshe bayan kammala horon zai za a baya da shedar digiri.

Zuwa ranar 31 ga watan Agusta da muke ciki ne za a kammala rijistar dukkanin mutanen da suke bukatar shiga shirin.

3736588

 

 

 

 

 

captcha