IQNA

23:53 - August 16, 2018
Lambar Labari: 3482898
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kungiyar fafutkar neman kawo karshen killace zirin Gaza Bassam Munasirah ya jaddada cewa, za su ci gaba da jerin gwano har sai an kawo karshen killace yankin Gaza baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a garin Gaza, Bassam munasira ya bayyana cewa, al'ummar gaza suna da hakkin su rayu kamar sauran al'ummomi na duniya, a kan haka killace yankinsu da Isra'ila ke yi baya a kan ka'ida.

Ya ce jerin gwanon da suke yi na neman ganin Falastinawa da aka kora daga yankunansu sun dawo, zai ci gaba har sai an janye takunkumin da aka kakaba wa al'ummar zirin Gaza, domin a cewarsa wannan killacewa na amatsayin laifin yaki da kuma keta hurumin 'yan adam.

Haka nan kuma Bassam ya yi kira ga sauran kungiyoyi masu fafutuka na kasa da kasa da su ci gaba da yunkurinsu domin ganin an kawo karshen zaluncin killacewa da ake yi wa mutane miliyan biyu da suke rayuwa a zirin Gaza.

3739041

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: