IQNA

Iran Ta Sanar Da Cewa A Shirye Take Ta kara Fadada Alakarta Da Musulmi Ethiopia

23:23 - August 27, 2018
Lambar Labari: 3482929
Bangaren kasa da kasa, Iran ta sanar da cewa za ta kara fadada alakarta da muuslmin kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun musulunci a Iran ya bayar da bayanin cewa, babban malamin addini na kasar Habasha Sheikh Umar Idris ya kai wata ziyara a a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Addis Ababa.

Bayanin ya ce shehin malamin tare da tawagarsa suka gana da jakadan Iran a kasar ta Habasha Sayyid Hassan Haidari, inda ya bayyana jin dadinsa dangane da irin taimakon da kasar ta Iran take baiwa cibiyoyin addinin muslunci na kasar.

A nasa bangaren jakadan na Iran a Habasha ya jaddada cewa, babu wani shamaki a tsakaninsu da musulmin kasar Habasha, kuma za su ci gaba da kara karfafa alakar da ke tsakaninsu.

Haka nan kuma jakadan an Iran ya yaba matuka da irin kyakkyawar alaka da jituwa da ke tsakanin musulmi da da kirista na kasar Habasha, tare da bayyana hakan a matsayin babban abin koyi ga al'ummomin duniya masu son zaman lafiya.

3741545

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha