IQNA

Dole Ne A Hukunta Sojojin Myanmar Kan Kisan Musulmin Rohingya

23:29 - August 27, 2018
Lambar Labari: 3482930
Kwamitin kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya ya kammala dukkanin bincikensa kan rahotannin da ya harhada kan kisan gillar da aka yi wa musulmin Rohingya a kasar Mayanmar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan kammala aikin binciken a yau kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yanke hukuncinsa na karshe, wanda ke tabbatar da cewa sojojin gwamnatin Myanmar su ne suka aikata kisan kiyashi a kan musulmin Rohingya.

Kwamitin ya bukaci majalisar dinkin duniya da ta dauki mataki na hukunta manyan jami'an sojin kasar Myanmar a gaban kotun manyan laifuka ta duniya, sakamakon laifin yaki da suka aikata kan fararen hula 'yan kabilar Rohingya, tare da yi ma mata fyade da kuma kisan gilla a kan sauran fararen hula da suka hada da kananan yara.

Haka nan kuma bayanin kwamitin ya ce babu wani abin da zai wanke rundunar sojin kasar Myanmar daga wannan laifi, domin kuwa za a mika batun ga manyan alakalan kotun manyan laifuka ta duniya domin yin dubi da kuma daukar mataki na gaba.

3741738

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :