IQNA

Mutane 30,000 Ne Suka Halarci Babban Taron Musulmin Amurka

22:47 - September 02, 2018
Lambar Labari: 3482945
Bangaren kasa da kasa, Musulmin kasar Amurka sun fara gudanar da zaman taronsu da suka saba gudanarwa a kowace shekara a birnin Houston.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Chron.com ya bayar da rahoton cewa, babbar kungiyar musulmi ta Amurka ta fara gudanar da taronta a karo na hamsin da biyar a birnin Houston na jahar Texas, wanda a kowace shekara ake gudanar da shi a jahohi daban-daban na Amurka. Taron yana samun halartar mutane fiyr da dubu talatin daga sassa na kasar Amurka, inda ake gabatar da jawabai da kuma baje kolin kayayyakin al'adu da suka shafi musulunci.

Babban abin da aka fi mayar da hankali a kansa a wurin taron dai shi ne kara wayar da kan musulmi kan hakikanin koyarwar addinin muslucni, nuna kyawawan dabi'u da suka hada da yin riko da gaskiya a cikin dukkanin lamari, da taimaka ma marassa karfi, da kawo sulhu da zaman lafiya a cikin jama'a.

A wannan karon an samu wasu masu adawa da musulmi da suka gudanar da gangami a kusa da wurin da ake taron, domin nuna rashin amincewa da duk wani abu da musulmi za su gudanar a cikin Amurka.

Dark Green wani Ba'amurke ne farar fata, wanda shi ne yake jagorantar masu adawa da taron, amma musulmi da suke taro a wurin suna ci gaba da gudanar da lamrinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, ba tare da sun kula da masu adawa da gudanar da taron ba.

3743302

 

 

 

 

 

captcha