IQNA

An Girmama Wadanda suka Gudanar Da Gasa Mai Taken (Annabin Rahma) A Uganda

23:17 - September 04, 2018
Lambar Labari: 3482951
Bangaren kasa da kasa an girmama wadanda suka gudanar da wata gasa mai taken Annabin Rahma a kasar Uganda wanda ofishin jakadancin Iran ya shirya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labarai na cibiyar bunkasa ala’adun musulunci a Iran ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da bikin girmama wadanda suka gudanar da wata gasa mai taken Annabin Rahma a kasar Uganda wanda ofishin jakadancin Iran ya shirya a kasar ta Uganda.

Wakilin cibiyar yada al’adin musluni Muradha Murtedhwi da jakadan Iran a Uganda Ali Bakhtiyai, Janaral Musa Ali mataimakin firayi ministan kasar Uganda, sheikh Ali Wasuwa mataimakin babban malamin addinin na kasar, da kuma shugaban jami’a Uganda da malaman jami’a da kuma malaman addini manyan masana na kasar fiye da 200 ne suka halarci wurin wannan taro.

Ita dai wannan gasa an shirya ta ne domin yin naari kan rayuwar manzon Allah (SAW) da kuma abubuwan da ya koyar da al’ummar musulmi, na daga kyawawan halaye da bautar Allah, da kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma.

Haka nan kuma gasar ta tabo wasu bangarori da suka shafi rayuwarsa yadda yake yin riko da addini isa umarnin Allah, da kuma yadda ya zama abin koyi a tsakanin dukkanin mabiya addinai, saboda halayensa abin koyi ne ga kowa.

3743947

 

تجلیل از برگزیدگان «جایزه پیامبر رحمت» در اوگاندا

تجلیل از برگزیدگان «جایزه پیامبر رحمت» در اوگاندا

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha