IQNA

An Kammala Gasar Kur’ani Mai Tsarki A Najeriya

23:05 - October 15, 2018
Lambar Labari: 3483040
Bangaren kasa da kasa, An kammala gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar tarayyar Najeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jaridar daily Trust ta bayar da rahoton cewa, an kammala gasar karatun kur’ani mai tsarki karo na ashirin da biyu da aka gudanar a garin Mina na jahar Neja a Najeriya, tare da halartar wasu daga cikin wakilan kasashen Afrika ta yamma.

Rahoton ya ce Umar Abdullahi daga jahar Jigawa shi ne wanda ya lashe wannan gasar, wadda aka gudanar da ita a bangaren tilawa da kuma kyawun sauti, gami da kiyaye hukuncin karatun kur’ani.

Kungiyar Izala ce dai ta dauki nauyin shirya wannan gasa ta karatun kur’ani mai tsarki.

Sheikh Muhammad sani yahya Jingir, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin rufe gasar, ya bayyana cewa manufar wannan gasar kur’ani ita ce, kara karfafa gwiwar musulmi musamman ma matasa, kan sha’anin kur’ani mai tsarki.

3756041

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :