IQNA

23:57 - October 16, 2018
Lambar Labari: 3483046
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin gudanar da wani babban taro na arbaeen a birnin Nairobi na kasar Kenya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun musulmunci cewa, yanzu haka an fara shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na arbaeen a birnin Nairobi na Kenya wanda shi ne irinsa na farko.

Bayanin ya ce karamin ofishin jakadancin Iran na kasar Kenya ne zai dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da taron, wanda zai samu halartar manyan baki da suka hada malaman adini na musulmi da kiristoci.

Kamar yadda kuam wasu daga masana da malaman jami’oi za su halarta, kuma wasu daga cikinsu za su gabatar da kasidu kan sadaukantarwa da Imam Hussain (AS) da kuma darussan da suke cikin gwagwarmayarsa.

3756297

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kenya ، nairobi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: