IQNA

Sabbin Makarantun Kur’ani Guda A Yankin Sinai

23:39 - October 25, 2018
Lambar Labari: 3483074
Bangaren kasa da kasa, an kafa makarantu 6 na kur’ani yankin arewacin Sinai da ke kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na mamlaka ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta samar da makarantun kur’ani guda 6 a arewacin kasar.

Muhammad Mukhrat Juma’a ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar ta Masar ya bayyana cewa, tuni wadannan makarantu suka fara gudanar da ayyukansu na koyarwa.

Ya ce babbar manufar samar da wadannan makarantu dai ita ce, kokarin kawo sabon salon a koyarwa tare da wayar da kan daliban kan hakikanin koyarwar kur’ani, domin hana akidar ta’addanci ci gaba da yaduwa  awannan yanki.

3758812

 

 

 

 

 

 

captcha