IQNA

Pompeo: Har Yanzu Saudiyya Bata Bayar Da Gasashiyar Amsa Kan kisan Khashogi Ba

23:58 - November 01, 2018
Lambar Labari: 3483091
Bangaren kasada kasa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeoya bayyana cewa har yanzu Saudiyya ba ta bayar da wani gamsashen bayani ba kan kisan gillar da aka yi wa Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Lebanon 24 ya habarta cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeoya bayyana cewa har yanzu Saudiyya ba ta bayar da wani gamsashen bayani ba kan kisan gillar da aka yi wa Khashoggi a cikin ofishinta da ke Turkiya.

Ya ce ya tattauna da dukaknin bangarorin na Saudiyya da kuma Turkiya danganeda bicike da ake gudanarwa kan kisan gillar da aka yi Khashogi, amma har yanzu akwai tambayoyi masu tarin yawa da mahukuntan saudiyya ya kamata su amsa  akan wannan batu, kuma sun ki amsa su.

Daga karshe ya ce duk da cewa akwai kyakyawar alaka da aminci tsakanin Amurka da Saudiyya, amma duk da haka Amuka za ta ci gaba da matsa lamba  akan wannan batu.

3760363

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، saudiyya ، amurka ، tsakanin ، Khashoggi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha