IQNA

23:54 - November 06, 2018
Lambar Labari: 3483105
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Australia sun gudanar da zaman taron tunawa da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, musulmin kasar Australia sun gudanar da zaman taron tunawa da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW).

Wannan taro dai ya gudana ne a birnin Perth na kasar ta Australia, inda za a gabatar da jawabai kan tarihin rayuwar manzon Allah (SAW) da kuma abubuwan da ya hadu da sua  cikin rayuwarsa mai albarka.

A kan gudanar da taron a kowace rana ta ashirin da takwas ga watan safar, wadda ta yi daidai da ranar wafatin manozn Allah (SAW) bisa ruwayoyi mafi inganci.

3761758

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: