IQNA

22:51 - November 07, 2018
Lambar Labari: 3483108
Bangaren kasa da kasa, Mata biyu da suka tsaya takarar neman kujerun majalisar wakilaia Amurka sun samu nasarar lashe zaben a jahohinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, majalisar shawara ta musulmin kasar Amurka ta nuna farin cikinta matuka dangane da nasarar da wadannan 'yan takara musulmi guda biyu suka samu.

'Yan takarar biyu su ne Rashida Tulaib da kuma Ilhan Umar, dukkansu sun tsaya ne a karkashin inuwar jam'iyyar Democrat, inda suka kayar da 'yan takarar jam'iyyar Republican mai mulki a kasar ta Amurka.

Ihan Umar dai 'yar asalin kasar Somalia ce da iyayenta suka yi gudun hijira zuwa Amurka tun tana da shekaru 12 da haihuwa, kuma ta tsaya takara ne a jahar Minnesota.

Ita kuma Rashida Tulaib 'yar asalin Palastine ce, kuma  ta tsaya takara ne a jahar Michigan, inda za su kasance mata musulmi na farko da za su shiga majalisar dokokin kasar Amurka.

Jam'iyyar Democrat dai a wannan zaben ta kwace rinjaye a majalisar wakilan kasar ta Amurka, inda jam'iyyar Republican ta Donald Trump ta sha kayi.

3762144

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Michigan ، amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: