IQNA

Musulmin Najeriya Ba Su Amince Da Takura Ma Mata Kan Hijabi Ba

20:32 - November 19, 2018
Lambar Labari: 3483134
Majalisar musulmin Najeriya ta jaddada cewa hakkin mata musulmi ne su sanya hijabi daidai da yadda addininsu ya umarta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kakakin majalisar muuslmin najeriya Salihu Shehu ya bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya a hana musulmi mata saka hijiabi a Najeriya,a  wurin aiki ko a makarantu a ko kuma wuraren hadahadar jama'a.

Ya ce majalisar musulmin Najeriya za ta yi tsayin daka domin kare hakkokin musulmi a duk inda suke a kasar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

A cikin wannan makon ne wata makaranta ta hana dalibai mata saka hijiabin muslucni a cikin jahar Oyo, lamarin da ya fusata musulmi da dama a jahar.

Akasarin al'ummar Najeriya dai mabiya addinin muslunci ne, baya ga su kuma sai mabiya addinin kirista da dai sauran addinai na gargajiya, kamar yadda kuma Najeriya ce kasar fata mafi girma  a duniya, wadda take da mtane kusan miliyan dari biyu.

3764961

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، hijabi ، Oyo
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha