IQNA

An Ware Wani Kasafin Kudi Domin Yaki Da Kyamar Addini A Makarantun Jamus

19:59 - November 20, 2018
1
Lambar Labari: 3483140
Ma'aikatar kula da harkokin iyalai ta kasar Jamus ta sanar da cewa, tav ware wani kasafin kudi na musamman domin yaki da kyamar addinai a makarantun kasar.

Kamfanin dillancin labaran Anadol ya bayar da rahoton cewa, Farncisca Giffy minister mai kula da harkokin iyalaia  kasar Jamus ta bayyana cewa, bisa la'akari da yadda kyamar addinai ke karuwa a cikin makarantun kasar, hakan ya sanya ala tilas ma'aikatarta ta dauki matakin da ya dace.

Ta ce wannan lamari ne da yake bukatar aiki na hadin gwiwa a tsakanin ma'aikatarta da sauran ma'aikatu, musamman ma ma'ikatr ilimi ta kasar.

Kasar Jamus na daga cikin kasashen da musulmi suka fi yawa a tsakanin kasashen nahiyar turai, amma a cikin shekarun baya-bayan nan musulmi suna fuskantar matsaloli na tsangwama, musamman a yankunan da ma su tsatsauran ra'ayin kiyayya da baki suke.

3765461

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
May allah help us on this work.
captcha