IQNA

23:43 - November 25, 2018
Lambar Labari: 3483150
Dakarun kasar faransa sun sanar da kashe wani babban jigo a cikin jagororin 'yan ta'adda masu da'awar jihadi a Mali.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Alwatan ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar Faransa da ke gudanr da ayyukan yaki da ta'addanci a kasar mali ta fitar, ta tabbatar da cewa an halaka Amadou Kufa, daya daga cikin manyan jagororin 'yan ta'adda a kasar.

Bayanin ya ce, dakarun na kasar Faransa sun kaddamar da farmaki a wasu sansanonin 'yan ta'adda a dararen Alhamis da Juma'a a yankin Ripar da ke arewacin Mali, kuma an kashe 'yan ta'adda kimanin talatin, daga cikinsu har da Ahamdou Kufa, mataimakin jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta Nustarul Islam.

Wannan kungiya dai tana daga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar alka'ida da suke kaddamar da munanan hare-hare a cikin kasar ta Mali da kuma makwabciyarta Burkina Faso.

3766850

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: