IQNA

Sheikhul Azhar Ya Taya Paparoma Munar Kirsimati

23:53 - December 18, 2018
Lambar Labari: 3483227
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib Babn malamin cibiyar Azhar ya taya Paparoma Francis murnar sallar kirsimati.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai Skynewsarabia ya bayar da rahoton cewa, a yau malamin cibiyar Azhar ya taya Paparoma Francis murnar sallar kirsimati da ma dukkanin kiristoci na duniya baki daya.

Ahmad Tayyib ya isar da wannan sako ne a yayin wata ganawa da suka yi yau tare da Paparoma Francis ta wayar tarho, inda ya ce yana fatan zai hadu da Paparoma a wurin taron addinai a hadaddiyar daular Larabawa.

A cikin makonni biyu masu zuwa ne dai ake sa ran za a gudanar da wani taro na mabiya addinai na duniya a birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda kuma ake sa ran Paparoma zai halarta.

Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarki Dubai kuma mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, za su yi farin ciki idan Paparoma ya halarci taron, domin kara habbaka dangantaka tsakanin musulumi da kirista.

3773549

 

 

 

 

captcha