IQNA

Aikewa Da Masu Sanya Ido A Kasar Yemen

23:54 - December 19, 2018
Lambar Labari: 3483231
Bangaren kasa da kasa, Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana bukatar aikewa da masu sanya ido kan dakatar da bude a birnin Husaidah Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniyaya fadi a yau a birnin New York cewa, Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana bukatar aikewa da masu sanya ido kan dakatar da bude a birnin Husaidah na kasar Yemen cikin gaggawa.

Babban magatakardan na majalisar dinkin duniya ya kara da cewa, aikewa da masu sanya ido kan dakatar da bude wuta a Hudaidah zai taimaka matuka wajen ganin an samu lafawar rikici a cikin gundumar.

Dangane da halin da al'ummar yankin suke ciki kuwa, ya bayyana cewa babban abin da ke gaban majalisar dinkin duniya a halin yanzu shi ne tabbatar da cewa an shigar da kayan agaji cikin gaggawa a kasar ta Yemen, da hakan ya hada da abinci da kuma magunguna, wanda tashar Hudaidaidah ce hanyar shigar da wadannan kayayyaki.

Tun bayan da aka rattaba hannu a tsakanin bangarorins siyasar Yemen kusan makonni biyu da suka gabata, har yanzu Saudiyya na ci gaba da karya wannan yarjjeniya, ita take ci gaba da kai hare-hare a birnin na Hudaidah da sauran sauran biranen kasar ta sama da kasa.

 

 

3773809

 

 

 

 

 

 

captcha