IQNA

Musulmin Birtaniya Suna Taimaka Wa Marassa Galihu A Lokacin Kirsimati

23:37 - December 24, 2018
Lambar Labari: 3483249
Musulmin kasar Birtaniya sun shiga cikin sahun masu taimaka ma marassa galihu a kasar a lokacin gudanar da bukukuwan kirsimati a kasar, wadda mafi yawan al'ummarta mabiya addinin kirista ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bangaren ingishi na BBC ya bayar da rahoton cewa, musulmin birnin Liverpool a kasar Birtaniya, suna tara taimako da ya hada kayan abinci da sauran kayan masarufi na bukatar rayuwa, domin rabawa ga marassa galihu a lokacin da ake shirye-shirye-shiryen bukukuwan kirsimati.

Rahoton ya ce baya ga tamako na kayan abinci, akwai kayayyakin taimako da suka shafi kananan yara musamman wadanda iyayensu ba su da karfi.

Tun daga farkon watan Disamban nan ne aka fara tattara taimakon a masallacin Abdullah Qailam, masallaci mafi jimawa a kasar Birtaniya, wanda aka gina shi tun a cikin shekara ta 1887.

Steven Medelton daya ne daga cikin masu taimaka marassa galihu a birnin na Liverpool, wanda ya shiga cikin wannan shiri da musulmi suke gudanarwa a birnin, inda ya ce ko shakka babu abin da musulmi suke yi na taimaka ma marassa karfi ba tare da cewa wanda suke taimaka mawa musulmi ne ko kirista ba, hakan ya burge shi, kuma ya yi masa tasiri matuka, a kan haka ya shiga cikin musulmi ana gudanar da wannan aiki tare da shi.

3774787

 

captcha