IQNA

Zaman Ta’ziyar Ayatollah Shahrudi Tare Da Halartar Jagora

23:58 - December 27, 2018
Lambar Labari: 3483256
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taaziyyar marigayi Ayatollah Shahrudia  husainiyar Imam Khomeni tare da halartar jagora.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da zaman taaziyyar marigayi Ayatollah Shahrudia  Husainiyar Imam Khomeni tare da halartar jagora da wasu daga cikin manyan malamai.

Haka nan kumada dama daga cikin dangi da abokan malamin sun halarci wurin ta’aziyyar, inda aka karanta kur’ani mai tsarki ga ruhinsa, tare da yi masa addu’a Allah ya jikansa da rahma.

Ayatollah Hashemi Shahrudi dai ya kasance shi ne ttsohon alkalain alkalai na kasar Iran, kamar yadda kuma ya kasance shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci a kasar, ya rasu a ranar Litinin da ta gabata, bayan fama da rashin lafiya.

3776129

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha