Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton wanda jaridar Wall Street Journal ta harhada kan makomar muhimman wuraren tarihi a kasar Yemen, ta tabbatar da cewa, sakamakon hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa akasar, an rusa da dama daga cikin muhimman wuraren tarihi na asar, musamman ma dadaddun masallatai da aka gina tun shekaru fiye da dubu daya da suka gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wadannan hare-hare ana kaisu ne bisa gangaci, da nufin rusa duk wani abu na tarihi da ke nuna tarihin kasar Yemen, wanda kuma majalisar dionkin duniya da UNESCO sun gargadi Saudiyya kan hakan, amma saboda goyon bayan Amurka da take samu a kan yakin, tana ci gaba da yin kunnen uwar shegu da wadannan kiraye-kiraye.
A cikin wani rahoto da hukumar kididdiga kan hasarorin da hare-hare Saudiyya suka jawowa kasar Yemen ta fitar a birnin sana'a, alkalumman hukumar sun nuna cewa a cikin shekaru uku da Saudiyya ta kwashe tana kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da ta ruwa akan al'ummar kasar Yemen, baya ga asarar rayukan dubban fararen hula da kaddarori masu tarin yawa, hakan kuma yayi sanadiyyar rushewar masallatai fiye da dubu biyu da dari biyu a kasar, da suka hada da masu tsohon tarihi a cikin addinin musulunci.