Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya jiragen yakin rundunar sojin kasar Iraki sun kaddamar da hare-hare har sau 30 a kan wasu wurare buyar mayakan 'yan ta'adda na kungiyar a cikin lardin Anbar.
Rahoton ya ce bisa ga bayanan da rundunar sojin Iraki ta bayar da kan batun, an kaddamar da hare-haren na jiya ne bayan samun cikakkun bayanai na asiri, kan yadda 'yan ta'addan an daesh suke kai komo a wuraren.
A lokacin kaddamar da farmakin an samu nasarar halaka wasu daga cikin 'yan ta'addana lokacin da suke hankoron tserewa, an kuma rugurguza dukkanin wuraren buyar tasu, tare da bata tarin makamai da suke a cikin wuraren.