IQNA

17:36 - February 04, 2019
Lambar Labari: 3483346
Bangaren kasa da kasa, kwamitin tsaron majalisar dinkin dniya ya gudanar da zama kan batun Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a jiya kwamitin tsaron maalisar dinkin duniya ya gudanar da wani zama na musamman kan batun halin da ake ciki a Palastine.

Rahoton ya ce wannan zama ya hada dukkanin mambobin kwamitin su goma sha biyar, inda suka tattauna kan abubuwan da suka wakna  baya-bayan nan a tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma Faastinwa.

Daga cikin abubuwan da zaman ya yi dubia  kansu akwai jerin gwanon da ake gudanarwa  akowace juma’aa cikin yankin zirin Gaza da kuma irin matakan da Isra’ila take dauka na yin kisan gilla a kan fararren hula masu jerin gwanon na lumana.

Duk da cewa Amurka taki amincewa da kuduror da dama da ake dauka domin takawa Isra’ila urki kan irin wadannan matakai da take dauka, amma saura mambobin kwaitin suna goyon bayan dakatar da Isra’ila daga kisan kiyashin da take yi wa Falastinawa.

3787312

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، mambobin ، takawa ، Falastinawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: