IQNA

23:56 - February 07, 2019
Lambar Labari: 3483355
Bangaren siyasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martini dangane da furucin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin jawabinsa ga manema labarai, Bahram Qasemi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martini dangane da furucin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan kasar Iran na cin fuska.

Qasemi ya ce bababr manufar Amurka a kowane lokaci ita ce shimfida ikonta a kan kasashe da al’ummomin duniya, wanda kuma kasashe masu yancin siyasa ba za su taba zama bayi ko ‘yan amshin shata ga Amurka ba,wanda Iran tana daga cikin wadannan kasashe da suke yin alfahari da ‘yancin siyasa da suke shi.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin matsalar da Amurka take da ita da Iran ba wani abu ba ne illa Iran bat a yarda ta zama ‘yar amshin shata ga Amurka ba, kamar yadda wasu kasashen yankin suka zama haka, inda suke samun kariya ta siyasa ta soji daga Amurka saboda sun mayar da kansu bayi a gar eta suna neman yarda da kariya daga gare ta.

Dangane da yadda shugaban Amurka yake bayyana Iran a matsayin kasar dab a ta bin tsarin dimokradiyya da kuma tauye hakkin bil adama, Qasemi ya ce Trump yana yin wannam furuci na rashin kan gado a kan Iran,a  daidai lokacin da yake kumfan baki wajen kare sarakuna da shugabannin wasu kasashe ‘yan kama karya a gabas ta tsakiya, wadanda ba su san wani abu wais hi akwatin zabe ba, balantana hakkin dan kasa ko dan adam.

Daga karshe ya ce duk wani matsin lambar Amurka ba zai iya sanya Iran ta mika kai bori ya hau ba, domin kuwa ta zabi ta zama kasa mai ‘yanci komai tsanani da takura da takunkumi, maimakon ta rayu a karashin kaskanci da bauta.

3788187

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Qasemi ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: