IQNA

23:59 - February 07, 2019
Lambar Labari: 3483356
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslucni na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya mayarwa Trump da martini kan sukar kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da take zantawa da manema labarai jiya a birnin Bagadaza na kasar Iraki, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya a Iraki bayan ganawarta da Ayatollah Sistani, Jeanine Hennis-Plasschaert ta bayyana cewa, Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya mayarwa Trump da martini kan sukar kasar Iran da kuma neman sanya Iraki a cikin matsala.

Ta ce Ayatollah Sistani ya sheda mata cewa Trump ba shi da hakkin yin amfani da kasar Iraki domin cutar da wata kasa,kuma hakan ba a bu ne da al’ummar Iraki za su amince da shi ba.

Trump ya yi furucin cewa za su ci gaba da kasancewa a cikin kasar Iraki domin sanya ido akn kasar Iran, yana mai yin ishara dacewa sojojin Amurka da ke Iraki suna cikin kasar ne domin dakon Iran.

3788219

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: