IQNA

Ana Gudanar Da Bukukuwan Cika Shekaru Arba’in Juyi A Iran

16:57 - February 12, 2019
Lambar Labari: 3483364
Bangzren siyasa, al'ummar Iran ke bikin cikar shekaru 40 cif da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda aka samar a rana irinta yau.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bikin na bana dai ya sha bamban dana sauren shekaru, duba da iya shekarun da kasar ta kwashe kan wannan turba, duk da barazanar da take fuskanta daga wasu kasashen musamman Amurka, wacce ta bayyana cewa Iran din ba zata ga shekaru 40 ba na nasara juyin.

Kamar yadda aka saba a kowace shekara dai, al'ummar kasar ta Iran, na gudanar jerin gwano domin nuna goyon baya ga tsarin da kasar take a kansa.

A nan birnin Tehran dubun dubatar jama'a ne ke haduwa a dandalin 'yanci inda mahukuntan kasar ke jawabi. 

Kamar yadda kuma a sauran sassan kasar miliyoyin jama'a ke gudanar da irin wadannan taruka, tare da kara jaddada goyon bayansu ga juyin juya halin musuluncin.

Mirigayi Iman Khomeini, ya koma kasarsa a ranar 1 ga watan Fabrairu na shekara ta dubu da dari tara da sabain da tara bayan shafe dogon lokaci na zaman hijira a birnin Paris na kasar Faransa, wanda daga ranar kuma kasar ta zama bisa wani tsari da ban a sarauta ba.

3789159

 

 

 

captcha