IQNA

23:04 - February 16, 2019
Lambar Labari: 3483377
Bangaren kasa da kasa, an samar da wani sabon mashin ATM a kasar Malysia wanda za a rika yin amafani da shi wajen raba shinkafa ga mabukata a kasar Malysia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na freemalaysiatoday cewa, an samar da wani sabon mashin ATM a kasar Malysia wanda za a rika yin amafani da shi domin bayar da taimakon abinci.

Bayanin ya ce za a fara amfani da wannan sabon mashin a baban masallacin Kualalmpour fadar mulkin kasar Malaysia daga nan zuwa karshen wannan wata.

Kakin masallacin ya bayyana cewa, babbarmanufar samar da wannan hanya ita ce bayar da taimako cikin sauki ga mabukata.

Tun kafin wannan lokaci dai an jima ana tattauana yadda za a bullo da wannan shiri, wanda zai yanzu aka samu damar aiwatar da shi.

3790389

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، malaysia ، ATM ، shinkafa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: