IQNA

Taliban Ta Gargadi India Dangane Da Ci Gaba Da Kai Wa Pakistan Hari

21:31 - February 27, 2019
Lambar Labari: 3483409
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Taliban ta gargadi gwamnatin India dangane da ci gaba da kai wa kasar Pakistan hari, tare bayyana hakan a matsayin lamari mai matukar hadari.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fadi a yau cewa, idan har India ta ci gaba da kai wa Pakistan harin soji, to kuwa hakan zai haifar da matsaloli masu tarin yawa a yankin.

Ya ce daga cikin matsalolin da hakan zai haifar hard a yin mummunan tasiri ga tattaunawar sulhu da ake gudanarwa a kasar Afghanistan.

Gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa ta kakabo jiragen yakin kasar India guda biyu a cikin yankinta, kuma ta kame wani matukin jirgin sojin kasar India da ke tuka daya daga cikin jiragen.

A halin yanzu dai kasashen duniya suna ci gaba da yin kira ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa, kuma su rungumi zaman lafiya da hakuri da juna.

3793992

 

 

 

 

captcha