IQNA

An Bude Zaman Taron Nazari Kan Addinai A Birnin Tehran

23:10 - March 05, 2019
Lambar Labari: 3483425
Bangaren kasa da kasa, a yau Talata an bude taron karawa juna sani a birnin Tehran na kasar Iran da ke yin dubi kan mahangar addinai kan rayuwar zamantakewar al’ummomi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudamar da wannan zaman taro ne tare da halartar masana da malamai na mabiya adinin muslunci da kuma mabiya adinin kirista daga kasashen ketare.

Cibiyar bunkasa al’adun muslunci t kasar Iran tare da hadin gwiwar cibiyar bunkasa ayyukan majami’ar Katolika a kasar Jamus ne suka dauki nauyin shirya taron.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin bude taron, shugabana cibiyar bunkasa al’adun musulunci Muhammad Mahdi Taskhiri ya bayyana cewa, addini shi ne ya koyar da dan adam kyawawan dabiu da girmama bil adama da kare hakkokinsa da tsayar da adalci da rikon amana da gaskiya.

Ya kara da cewa, babu wani addini da ya yarda da gallazawa dan adam da cin zarafinsa da keta alfarmarsa, domin addini yana kare hatta dabbobi da tsirrai balantana dan adam, wanda shi ne halittar da Allah ya girmama fiye da dukkanin abin da ke doron kasa.

Shi ma a nasa bangaren Christian Strobel mamba a babbar cibiyar kula da majami’oin kiristoci mabiya darikar Katolika  a kasar Jamus ya fadi a wajen taron cewa, dukkanin addinai da suka imani da Allah kama da musulunci da kiristanci da yahudanci, ba su amince da shishigi kan bil adama ba, idan kuam wani ya yi hakan, to ba da sunan addinasa ya yi ba.

3795597

 

captcha