IQNA

21:54 - March 11, 2019
Lambar Labari: 3483445
Babbar cibiyar musulmin kasar Birtaniya na shirin gudanar da bababn taronta na shekara-shekara domin yin dubi kan muhimman lamurra da suka shafi musulmi da suke rayuwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A cikin wani bayani da cibiyar ta fitar a shafinta na yanar gizo ta sanar da cewa, tana cikin shirin gudanar da babban taron na wanann shekara, wanda zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar ta Birtaniya.

Taron dai wanda akasari masana ne suke halartarsa da kuma wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar gami da kuam wakilan kungiyoyi daban-daban a kasar , da suka hada da na malaman jami’oi da kuma na farar hula, yakan  mayar da hankali kan abubuwan da suke a matsayin kalu bale a cikin lamurran zamantakewa da kuma yadda za a fuskance.

Haka nan kuma wasu daga cikin masana musulmi sukan gabatar da jawabai dangane da matysayar musulmi a kan abubuwa da dama da suke shigewa jama’a dubu dangane da musulunci musamman ga wadanda ba musulmi ba, da kuma yadda za a kara samun kyakkayawar fahimtar juna da alaka mai kyau tsakanin musulmi da sauran al’ummar Birtaniya.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi akwai manyan malamai daga jami’oin Oxford, Bristol, London, Birmingham da sauran su.

 

3796926

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: