Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wadanda suka sace Ahmad Sulaiman fitaccen makarancin kur’ani a Najeriya suka yi garkuwa da shi sun sake shi, bayan kwashe tsawon lokaci a hannunsu.
Bayan sakinsa Ahmad Sulaiman ya bayyana cewa, sun sha wahala a wurin da aka tsare su, amma daga karshe dai sun kubuta.
Rundunar sojin jahar Katsina ta bayyana cewa ta taka gagarumar rawa wajen kwato Ahmad Sulaiman da wadanda aka yi garkuwa da su tare da shi.
Ana fuskantar matsaloli na garkuwa da jama’a a tarayyar Najeriya musamman a cikin jahohin Katsina a Zamfara da wasu yankunan kasar.
Wanann matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da gwamnatin kasar ta ce tana yin iyakacin kokarinta domin magance ta, kasantuwar hakan yana adabar jama’a da dama da ba su ji ba su gani ba.