IQNA

Rasha Ta Ce Tana Kokarin Ganin An Warware Rikin Libya Ta Hanyar Tattaunawa

20:21 - April 09, 2019
Lambar Labari: 3483536
Gwamnatin kasar Rasha ta sanar a jiya itinin cewa, tana yin iyakacin kokarinta domin ganin an waware rikicikin da ya kunno kai kasar Libya ta hanyar ruwan sanyi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin Moscow, kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana cewa, abin da yake faruwa a kasar Libya lamarin da ke bukatar a kai zukata nesa, domin shawo kansa ta hanyoyi na lumana.

Ya ce a halin yanzu Rasha ta dukufa wajen ganin ta gamsar da dukkanin bangarorin biyu kan su dakatar da bude wuta, kuma su rungumi hanyar tattaunawa domin warware matsalolinsu.

Kakakin fadar Kremlin ya kara da cewa, wani da ya zama wajibi a kan dukkanin bangarorin biyu shi ne su nisanci duk wani abin da zai iya jawo asarar rayukan fararen hula a ciki da wajen birnin Tripoli.

A nata bangaren babbar jami’a mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai ta fadi a zaman taron ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar turai jiya a Burussels cewa, kungiyar tarayyar turai na kiran dukkanin bangarorin da ke rikici a Libya da su dakatar da bude wuta, domin samun damar gudanar da ayyukan jin kai a birnin Tripoli da kewaye.

3801995

 

 

captcha