IQNA

23:56 - April 28, 2019
Lambar Labari: 3483587
Rahotanni daga Libya na cewa iyalai fiye da dubu 39 ne suka kauracewa babban birnin kasar Tripoli, sakamakon rikicin da ake yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Rusia yaum ta bayar rahoton cewa,  Stefan Djuric kakakin UN ya ce, iyalai fiye da dubu 39 ne suka kauracewa babban birnin kasar Tripoli, sakamakon rikicin da ake yi, tsakanin dakarun gwamnatin kasar da kuma dakarun da ke neman kwace birnin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya assabar hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta ce daga lokacin da dakarun sojin kasar suka fara kai hari birnin Tripoli zuwa yanzu kimanin Mutane dubu talatin da tara, suka yi hijra daga birnin.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya na cewa hare-haren da dakarun haftar ke kaiwa birnin Tripoli ya yi sanadiyar katsewar wutar lantarki, ruwan sha, karamcin abinci da magani da kuma man fetir a yankunan dake kewaye da birnin.

An kirayi al’ummar birnin das u zama cikin shirin kare shi daga hare-hare.

 

 

3806875

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Haftar ، Libya ، Tripoli
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: