IQNA

23:00 - May 04, 2019
Lambar Labari: 3483604
Bangaren kasa da kasa, an kame tsoffin manyan daraktoci na hukumar leken asirin kasar Aljeriya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, an kame tsoffin manyan daraktoci na hukumar leken asirin kasar Aljeriya, wato Muhamamd Madin da  kuma Bashir Tartak., bayan nan kuma an kame Sa'id Butaflika dan uwan tsohon shugaban kasar ta Aljeriya Abdulazizi Butaflika.

Rahoton ya ce majiyoyin tsaro sun bayyana cewa a yau Lahadi za a mika su ga bangaren shari'a.

Kafin wanann lokacin Ahmad Qaeed Saleh babban hafsan hafsoshin sojin kasar Aljeriya ya bayyana cewa, zai gudanar da bincike na gaskiya kan batun masu laifin cin hanci da rashawa.

Ya jadda cewa ba zai daga wa kowa kafa ba kan batun cin hanci da rahawa a kasar.

3808741

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Aljeriya ، Butaflika
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: