IQNA

22:53 - May 05, 2019
Lambar Labari: 3483608
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, Iran tana yin Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, hare-haren da Isra’ila take kaiwa al’ummar zirin Gaza abin yin tir da Allawadai ne.

Ya ci gaba da cewa wadannan hare-hare na ta'addanci sun yi sanadiyyar shahadar fararen ula da suka hada da mata da kananan yara, amma kasashen da suke kare manufofin yahudawa sun yi gum da bakunansu.

Dangane da nauyin da ya rataya kan sauran kasashe kuwa, ya bayyana dukkanin kasashen duniya masu sauran lamiri da masu 'yancin siyasa, ya kamata su dauki matakan da suka dace domin takawa yahudawan sahyuniya birki kan wannan ta'asa.

3809073

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: