IQNA

0:01 - May 09, 2019
Lambar Labari: 3483620
An fara gudanar da babbar gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa tare da halartar kasashe 90.

Kamfanin dillancin labaran iqna, An fara gudanar da babbar gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa tare da halartar kasashe 90.

Ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani mafi girma a birnin na Dubai wadda aka fara gudanarwa a jiya Talata, wadda kuma za ta kawo karshe a ranar 14 ga watan Rmadan mai alfarma tare halartar kasashe 90.

Rahoton ya ce dukaknin mahalrta gasar dai wadanda suka samu matsayi a gasar da aka gudanara  cikin kasashensu ne, domin su zama wakilai a wannan babbar gasa.

Mahardata kur’ani mai tsarki su 230 ne suke halartar wannan gasa daga kasashen duniya daban-daban, inda a jiya suka fara karawa da juna, kuma za a ci gaba da gasa har zuwa sha hudu wannan wata na ramadana mai alfarma.

Ahmad Zahed shi ne shugaban kwamitin da ke daukar nauyin shirawa da kuma gudanar da gasar, ya bayyana cewa sun yi kyakkawan shirin gudanar da gasar tare da daukar nauyin dukkanin baki da suke halarta.

Wannan gasa cibiyar Juma’a majed ke daukar nauyin shiryata da gudanar da ita tsawon kimanin shekaru ashirin da biyar da suka gabata, kuma ya zuwa wannan cibiya ta buga littafan adini kimanin dubu 250 zuwa dubu 300 da kuma majallu na musulunci kimanin dubu 6 da ake rabawa a kasashen musulmi.

 

 

3809977

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: