IQNA

23:49 - May 11, 2019
Lambar Labari: 3483628
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wata gasar kur'ani mai sarki a tarayyar Njeriya a birnin Abuja fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bangaren yada labarai na ma'aikatar kula da al'adun muslucni ya sanar da cewa, Shifa Garba daya daga cikin jagororin kungiyoyin mata musulmi a Najeriya da kuma karamin jakadan Iran a kasar Sayyid Mahmud Azimi Nas-Abadi, sun tattauna batun fara gudanar da gasar.

Yanzu haka ana shirin gudanar da gasar kur'ani mai sarki a tarayar Njeriya a birnin Abuja a cikin wannan wata na ramadana mai alfarma.

Bayanin ay ci gaba da cewa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar musulucni ta Iran a birnin an Abuja ne ya shirya daukar nauyin wannan gasa, wadda za ta hada makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasar.

Tarayyar Najeriya wadda ita ce kasa mafi girma a nahiyar Afrika, na daga cikin kasashen da ake mayar da muhimamnci matuka wajen gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani mai tsarki musamamna  cikin watan ramadan.

Wannan gasa za ta kasance ne a matakai daban-daban, akwai mataki na hardar kur'ani baki daya, sai kuma masu hardar rabin kur'ani, da kuma  amsu rubu'i, bayan an kuma a kwai bangaren tilawa.

bayan kammala gasar wadda za ta dauki 'yan kwanaki ana gudanar da ita, za a bayar da kyautuka ga dukaknin wadanda suka halarci gasar, haka nan kuma za a bayar da wasu kyautukan na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazoa  yayin gudanar da gasar.

 

3810531

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، Abuja ، Najeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: