IQNA

23:59 - May 12, 2019
Lambar Labari: 3483634
Bangaren kasa da kasa, an kai harin ta'addanci a wata majami'a a Burkina Faso da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 6..

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ta'addancin ne  akan wata majami'ar mabiya addinin kirista a kasar Burkina Faso.

Rahoton ya ce maharan sun kai harin ne a lokacin da mabiya addinin kirista suke gudanar da iabada a cikin majami'ar tasua  jiya Lahadi, kuma an kashe babban malamin majami'ar tare da wasu mutane 6a  wurin.

Haka nan kuam rahoton ya kara da cewa 'yan bindigar sun bude wuta  akan wuraren jama'a da hakan ya hada da wani babban shagon sayar da magunguna, inda suka tarwatsa mutane, kuma suka banka wuta  akan wata motar daukar marassa lafiya.

jami'an tsaro sun ce adadin mutanen da suka kai harin ya kai mahara 20 zuwa 30.

3810987

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: