IQNA

23:49 - May 31, 2019
Lambar Labari: 3483689
Bangaren siyasa, Shugaba Hassan Rauhani na kasar Iran ya fadi yau cewa, makircin makiya al’ummar musulmi a kan Quds da Palestine ba zai taba yin nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da yake halartar jerin gwanon ranar Quds ta duniya a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau, shugaban kasar ta Iran Dr. Hassan Rauhani ya jaddada cewa, Iran ba za ta taba da baya ba wajen taimaka ma al’ummar Palestine.

Ya ce dukkanin matsin lamabar da Iran take fuskanta daga manyan kasashen duniya masu girman kai da yahudawa, sakamako ne na goyon baya da taimakon da Iran take baiwa al’ummar Palestine, wanda kuma ba zata taba ja da baya ba kan hakan, domin kuwa taimakon al’ummar Palastine batu ne na addini da ‘yan adamtaka.

Shugaba Rauhani ya kara da cewa, ranar Quds ta wannan shekara ta sha bamban da sauran ranakun quds da suka gabata, domin a wannan karon, Amurka da wasu masu ha’inci daga cikin kasashen larabawa, suna son mika Palestine ga Isra’ila a hukumance da sunan abin da suke kira da yarjejeniayr karni.

Ya ce a kan haka ne ma taken ranar quds ta duniya a wanann karo ya zama kan kin amincewa da makircin da ake kira yarjejeniyar karni, wanda kuma al’ummar Palastine da dukkanin al’ummomin larabawa da sauran al’ummomin musulmi an duniya ba su amince da wannan makirci ba, in ban da ‘yan kalilan daga cikin sarakunan larabawa.

 

3815962

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rauhani ، Iran ، ranar quds
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: