IQNA

23:59 - June 02, 2019
Lambar Labari: 3483702
Bangaren gungun daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan masallacin aqsa tare da lakada wa masu itikafi duka.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa a yau daruruwan yahudawan sahyuniya masu tsattauran ra’ayi sun kai farmaki kan masallacin Aqsa inda suka lakada wa masu itikafi a cikin masallacin  duka tare da jikkata wasu daga cikinsu.

Bayan isar yahudawan a cikin harabar masallacin aqsa mai afarma, sun amu matasan falastinawa a wurin, inda suka fara artabu da su kafin su shiga cikin masallacin.

Bayan da suka tarwatsa matasan da ke cikin harabar masallacin, tare da kame wasu, yahudawan tare da jami’an ‘yan sanadan Isra’ila da ke mara musu baya sun kusa kai ckin masallacin, bayan da suka balle babbar kofar masallacin.

Yahudawan sun yin amfani da sanduna wajen dukar dukkanin wadanda suka samua  cikin masallacin, da suka hada da masu itikafin wtan Ramadan, inda suka jikkata wasu daga cikin su kuma suka yi waje da su .

Yahudawa masu tsattauran ra’ayi na da imanin cewa, falastinawa sun mamae gabashin birnin Quds, kuma dole ne a kore su, tare da kwace masallacin aqsa daga hannun musulmi.

 

 

3816553

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: