IQNA

22:23 - June 15, 2019
Lambar Labari: 3483740
A Sudan an tuhumi hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al’bashir da laifukan cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wata sanarwa ce da masu shigar da kara suka fitar a jiya Alhamis aka tabbatar da hakan, inda a ciki aka nemi a soma tuhumar shugaban, da sojoji suka kifar da mulkinsa bisa matsin lambar masu zanga zanga, kamar yadda kamfanin dilancin labaren kasar na Sunna ya rawaito.

Wata majiya wacce ta bukaci kamfanin dilancin labaren na Sunna, ya sakaya sunanta, ta ce ana tuhumar Al-Bashir da mallakar kudaden waje, da dukiya ta hanyar da bata dace ba, da kuma bada umarnin ayyana dokar ta baci a kasar.

A ranar ashirin da daya ga watan Afrilu da ta gabata, shugaban mulkin sojin kasar, Janar Abdel Fattah Burhane, ya sanar da cewa, an gano kudade da yawansu ya kai sama da dala miliyan dari da sha uku  a gidan hambararen shugaban kasar.

3819574

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، Albashir
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: