IQNA

23:51 - June 21, 2019
Lambar Labari: 3483759
Bangaren siyasa, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa za su kai karar Amuka a gaban majalisar dinkin duniya kan shisshigin da ta yi a cikin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

a lokacin da yake Karin hase kan matakan da za su dauka dangane da shishigin da Amurka ta yi kan Iran ta hanyar aikewa da jirgin leken asiri a cikin yankin ruwan kasar, Zarif ya ce za su kai kara a kan batun a gaban majalisar dinkin duniya.
Zarif ya ce baya ga yakin tattalin arziki da Amurka ta kaddamar kan Iran, a halin yanzu kuma tana kokarin tsokanar Iran a bangaren tsaron kasarta, ya ce ba su neman kowa da yaki, amma za su kare kasarsu da dukkanin karfinsu a kan duk wani shishshigi da za a yi a kanta.
Ya kara da cewa, ikirarin da Amurka take yi na cewa Iran ta kakkabo jirginta a cikin yankin ruwa na kasa da kasa karya ce, kuma Iran za ta gabatawar majalisar dinkin duniya da dalilai kan hakan.

3821052

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Zarif ، Iran ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: