IQNA

23:50 - June 23, 2019
Lambar Labari: 3483766
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkokin musulmi a Najeriya ta bukaci da a kare hakkokin musulmi a jami’oi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar kare hakkokin musulmi a Najeriya MURIC ta fitar a ta bakin shugabanta Ishaq Akintola, ta yi kakausar suka kan take hakkokin wasu dalibai musulmi a jami’ar Adeleke.

Bayanin ya ce daga cikin matakan da jami’ar take dauka na taka hakkokin musulmi har da tilasta su zuwa coci a ranar lahadi tare da sauran dalibai kiristoci.

Baya ga haka kuma tun kafin wannan lokacin an hana dalibai mata muuslmi saka hijabia  cikin jami’ar, wanda a cewar kungiyar wannan ya sabawa tsarin doka na kasa da ‘yancin dan Najeriya.

Kungiyar ta kirayi hukumomin ilimi a kasar da su dauki matakan da suka dace domin takawa hukumomin wannan jami’a burki kan irin wadannan matakai da suke dauka.

 

 

3821449

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: