Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a cikin wani bayani bayani da ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta fitar a jiya, ta sanar da cewa, tana shirin bude ofishin jakadanci a Palestine domin nuna cikakken bayanta ga falastinawa.
Bayanin ya ce yanzu haka wata tagawar Oman na shirin tafiya birnin Ramallah na Falastine domin far shirye-shiryen bude ofishin jakadancin.
Wannan mataki na Oman na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin kasashen larabawa suka shagaltu a birnin Manama na Bahrain domin tattauna shirin yarjejeniyar karni, wanda ke nufin mika Falastinu ga mamayar Isra’ila a hukuamnce.