IQNA

23:54 - July 19, 2019
Lambar Labari: 3483857
Bangaren kasa da kasa, wasu fitattun mutane daga kasashe daban-daban na nahiyar turai sun bukaci a duba batun Sheikh Zakzaky.

Kamfanin dillancin labaran iqna daga kasar Afrika ta kudu ya bayar da rahoton cewa, wasu fitattun mutane daga kasashe daban-daban na nahiyar turai sun bukaci bin kadun lafiyar Sheikh Zakzaky da ake tsare da shi a Najeriya.

Mutanen sun hada da masu rajin kare hakkokin bil adama, da malaman jami’oi gami da masana a bangarori na shari’a da kiwon lafiya da dai sauransu.

Mutanen sun rubuta wasika wadda suka rattaba hannua  kanta, kuma suka aike da ita zuwa babban sakataren majalisar dinkin duniya, inda suke bukatar a bi kadun wannan batu.

Wannan dai ba shi ne karon karon farko da ake kama Sheikh Ibrahim Zakzaky a Najeriya ba, domin kuwa ko a lokacin mulkin Obasanjo na soji an kame shi, haka lokacin Shagari, da Buhari yana soji, da kuma okacin mulkin Babangida da Abacha.

A cikin watan Disamban 2015 ne sojoji suka kaddamar da farmaki a kan Husainiyar Baqiyyatollah da gidan Sheikh Zakzaky a garin Zaria, inda suka rusa gidan nasa da kuma kashe daruruwan jama’a, tare da kama shi, bisa zargin cewa magoya bayan Harkar Musulunci sun yi kokari kashe hafsan sojoji.

Ana iya karanta matanin English a nan: - 

 

3828220

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: