IQNA

23:50 - July 20, 2019
Lambar Labari: 3483859
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Masar sun rufe wata cibiyar muslucni bisa zarginta da alaka da ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa,a  jiya jami’an tsaron kasar Masar sun kai samamea  wata cibiyar muslucni da ke garin Mait Suhail da ke cikin gundumar Minyal Kamh, a cikin lardin Sahrqiyyah.

Wannan farmaki ya zo ne bisa zargin cewa wanann cibiya tana da alaka da wasu bangarorin ‘yan ta’adda, inda aka kae wasu mata uku da aka samua  wurin, wadanda aka sake su daga bisani.

Jami’an tsaron kasar ta Masar sun ce wannan na daga cikin irin matakan da suke dauka na yaki da ta’addanci a kasar.

Abin tuni dai a cikin wannan cibiya an gudanar da janazar mamaci ga tsohon shugaban kasar masar Muhammad Morsi, wanda ya rasua  lokacin da aka gabatar da shia  kotu a kwanakin baya a kasar ta Masar.

3828276

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، masallaci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: