IQNA

An Haramta Harkar Musulunci IMN A Najeriya

20:53 - July 29, 2019
Lambar Labari: 3483894
Gwamnatin tarayar Najeriya ta sami umurnin kotu na haramta harka islamiya ta Najeriya wacce aka fi saninta da IMN.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto shafin Aljazeera na cewa, bisa wani rahoto gwamnati ta dauki wannan matakin ne bayan da shugaban kasa yagana da manya-manyan shuwagabannin hukumomin tsaron kasar.
 
Labarin ya kara da cewa a jiya jumma’a ce dai gwamnatin ta sami wannan umurnin daga hannun mai shari’a Nkeonye Maha na wata babbar kotu a Abuja.
 
Umurnin kotun ya na cewa “ Daga yanzu babu wani mutum ko gungun mutane da suke da damar hulda da kungiyar ta yan shi’ar, hulda ta ko wacce iri ce”.
 
Jaridar ta kara da cewa “domin kammala aikin wannan umurnin, kotun ta bukaci babban jami’I ma’aikatar shariya ta kasa, wato antony janar na kasa, ya shelanta wannan umurnin a cikin manya-manyan jaridun kasar guda biyu. Kafin jaridar Premiumtimes dai, jaridar Punch ce ta fara buga labarin.
 
Zangar-Zanagar yayan wannan Harka dai tana zama ta tashin hankali, wanda yake kai ga rasa rayuka a cikin yan makonnin da suka gabata, inji jaridar.
 
Tun a cikin watan Disamban 2015  ne aka kama Sheikh Zakzaky, amma har zuwa 13 ga watan janairun  2018 ana ci gaba da tsare shia  wani wuri a cikin Abuja, kafin daga bisani a mayar ad shi Kaduna inda ake yi masa shari'a.
 
 
captcha