IQNA

23:56 - August 01, 2019
Lambar Labari: 3483901
Bangaren siyasa, Muhammad jawad Zarfi wanda Amurkan ta shigar da sunansa a cikin jerin sunayen mutanen da ta kakabawa takunkumi, ya bayyana cewa:

Kamfanin dillancin labaran iqna, Zarif ya bayyana cewa, “Ina gode muku da kuke dauka ta a matsayin wata babbar barazana ga manufofinku.”

Zarif ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Amurka ta kakaba mani takunkumi saboda ni ne mai Magana da yawun Iran a duniya, ashe fadar gaskiya yana da daci har haka?”

Zarif ya ci gaba da cewa; Ko kadan wannan takunkumin ba shi da wani tasiri akaina, ko iyalina, domin ba ni da kudi ko wata kaddara a wajen iyakokin Iran, don haka ina yi muku godiya da ku ka dauke ni a matsayin babbar barazana ga manufofinku.”

A jiya Laraba ne dai baitul Malin Amurka ya kakabawa Muhammad Jawad Zarfi takunkumi a matsayin ci gaba da siyasar matsin lamba akan al’ummar Iran.

Iran dai ta sha nanata cewa siyasar matsin lamba da Amurka take amfani da ita akanta ba za tilasta mata ba ta mika wuya.

 

3831628

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Zarif ، Amurka ، takunkumi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: